Connect with us

Labarai

Gwamnatin Tarayya za ta sake bude Iyakar kasar

Published

on

Gwamnatin Tarayyar ta amince da sake buɗe iyakar ƙasa ta Tsamiya da ke jihar Kebbi domin ci gaba da kasuwancin ƙetare iyaka, tare da sanya tsauraran matakan tsaro da bin ƙa’idoji.

 

Kwanturola-Janar na Hukumar Kwastam ta Nijeriya (NCS), CG Adewale Adeniyi, ne ya bayyana hakan a ranar Asabar yayin wata ganawa da masu ruwa da tsaki a jihar Kebbi, ciki har da ’yan kasuwa, masu safarar kaya da kuma ’yan kasuwar albasa.

 

Adeniyi ya ce matakin sake buɗe iyakar ya biyo bayan umarnin Gwamnatin Tarayya, inda ya jaddada cewa za a gudanar da kasuwancin ne cikin kulawa ta musamman domin tabbatar da tsaro da bin dokokin kwastam.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!