Kasuwanci
Gwamnatin Tarayyar ta soke lasisin kamfanonin hakar ma’adanai guda 1,263

Gwamnatin Tarayyar Najeriya, ta sanar da soke lasisin wasu kamfanonin hakar ma’adanai a kalla guda dubu ɗaya da dari biyu da sittin da uku (1,263) a fadin Najeriya.
Rahotonni sun nuna cewa, daukar wannna mataki ya biyo bayan kin biyan haƙƙoƙin gwamnati da kamfanonin suka dade ba su biya ba.
Ma’aikatar ma’adanai ta tarayya ta ce, daukar matakin zai taimaka wajen tsaftace fannin hakar ma’adanan, da kuma bai wa ƙwararru da masu bin ƙa’ida damar gudanar da ayyukansu ba tare da cikas ba.
Haka kuma gwamnati ta yi gargadi ga sauran masu lasisi da su tabbatar da biyan hakkokinsu domin kauce wa irin wannan matakin a nan gaba.
You must be logged in to post a comment Login