Labarai
Gwamnatin Tinubu ta aiwatar da sauye-sauye masu inganci- Atiku Bagudu

Ministan kasafin kudi da tsare-tsaren tattalin arziki, Atiku Bagudu, ya ce gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta aiwatar da sauye-sauye masu karfi da suka sanya tattalin arzikin Najeriya fara dawowa da kuma ci gaba mai dorewa, duk da radadin da ake fuskanta a baya.
Ministan ya bayyana hakan ne yayin da ya ke zantawa da manema labarai na fadar shugaban kasa bayan wata ziyarar girmamawa da ya kai wa shugaba Tinubu a gidansa da ke birnin Lagos.
Alhaji Atiku Bagudu, ya kuma yaba da manufofin tattalin arzikin gwamnatin, inda ya ce Najeiya ta fara cin gajiyar sauye-sauyen tsarin da aka dade ana jira.
You must be logged in to post a comment Login