Ƙetare
Gwamnatin Trump ta yi zargin ana yawan kashe Kiristoci a Najeriya

Gwamnatin Amurka karkashin Donald Trump, ta sake sanya Najeriya cikin jerin kasashe masu matsala ta musamman saboda zargin yi wa Kiristoci kisan kare dangi.
Wannan zargi ya biyo bayan jawabin da Mataimakin Shugaban kasa, Kashim Shettima, ya yi a taron Majalisar Ɗinkin Duniya a kwanan baya.
A lokacin taron Shettima ya bayyana halin da ake ciki a Gaza a matsayin abin tausayawa, inda ya hi kira da a tabbatar da zaman lafiya ta hanyar kafa kasashe biyu masu zaman kansu.
Bayan jawabin nasa, wasu kungiyoyi suka fara yada labarin cewa ana yi wa Kiristoci kisan kare dangi a Najeriya, duk da cewa mutane da dama sun musanta jita-jitar.
A ranar Juma’a, Trump ya wallafa wani rubutu a shafinsa na X, cewa Kiristoci na fuskantar barazana a kasar nan.
You must be logged in to post a comment Login