Ƙetare
Gwamnatin Turkiyya ta gargaɗi mahukuntan Najeriya game da ƙungiyar ta’addanci ta Fethullah

Gwamnatin kasar Turkiyya ta gargaɗi mahukuntan Kasar nan ya game da wata ƙungiyar ta’addanci mai suna Fethullah da ke fakewa a makarantu da asibitoci, yayin da tace nan ba da jimawa ba za ta fara kai hare-hare.
Jakadan kasar ta Turkiyya a Najeriya Mehmet Poroy, ne ya bayyana hakan, ya na mai cewa ƙungiyar ta na gudanar da ayyukanta a sauran sassan duniya ba wai Najeriya kadai ba.
Poroy na gabatar da wannan gargaɗi ne yayin bikin liyafar cin abinci ta musammn da aka shirya a ofishin jakadancin Turkiyya a Najeriya tare da Turkawa mazauna Najeriya don murnar ranar Dimokraɗiyya da kuma haɗin kai.
A cewar sa wannan ƙungiya tana da matuƙar haɗari kuma tana shirya ayyukanta a boye a sassan duniya, To sai dai wasu na ganin wannan farfaganda ce kawai ta siyasa da ke neman tsallake Turkiyya ta mamaye sauran sassan duniya da nufin shafawa fitaccen malamin ƙasar da ke gudun hijira yanzu haka a Amurka Fethullah Gulen kashin kaji.
Ƙungiyar mai take Fethullah ta yi fice a duniya wajen ayyukan jin ƙai da samar da makarantu a asibitoci a ƙasashen duniya, kuma irin waɗannan makarantu da cibiyoyin lafiya ne ƙasar ta Turkiyya take zargin suna amfani da su don ɓoye manufar su.
You must be logged in to post a comment Login