Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Gwamnatin Yobe ta rufe dukkannin makarantun kwanan jihar

Published

on

Gwamnatin jihar Yobe ta sanar da rufe makarantun kwana a jihar a wani mataki na kare dalibai sakamakon yawaitar sace daliban da ‘yan bindiga ke yi a jihohin arewacin kasar nan.

Kwamishinan ilimin jihar  Dr. Muhammed Idris ne ya bayyana haka a lokacin da ya ke ganawa da manema Labarai a Damaturu babban birnin jihar.

‘‘Mun bada umarnin rufe dukkannin makarantun sakandire ne don kare lafiyar daliban’’ a cewar Kwamishinan.

Kwamishinan ya kara da cewa, ma’aikatar ilimin za ta yi aiki da hukumomin tsaro da ke jihar don tabbatar da cewa an bada tsaron da ya dace a makarantun kafin komawar daliban.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!