Connect with us

Labarai

Satar Dalibai: Ganduje ya sake rufe wasu makarantun kwana.

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta bada umarnin rufe makarantun Tsangayu na kwana da ke fadin jihar.

A cewar gwamnatin, daukar wannan matakin na rufe makarantun Tsangayun na kwana yana alaka ne da sace ‘yan makarantar mata ta Jangebe da ke jihar Zamfara wadanda aka sako su a yau talata da kuma dalibai da aka sace a karamar hukumar Kagara da ke jihar Niger.

A cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugaban hukumar kula da makarantun Tsangayu na jihar Kano Gwani Yahuza Gwani Dan Zarga, ta ruwaito gwamnan na Kano na cewa, a baya-bayan nan gwamnati ta rufe makarantun kwana guda goma sha biyu a matsayin wani mataki na kare lafiyar dalibai.

“Gwamnati tana umartar iyayen yara da su gaggauta zuwa su kwaso ‘ya’yansu daga makarantun Tsangayar ba tare da bata lokaci ba” A cewar Gwamna Ganduje.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv

Now Streaming

Archives