Connect with us

Kiwon Lafiya

Gwmantain tarayya ta bukaci dakatar da dokar haramta kiwo barkatai

Published

on

Gwamnatin tarayya ta bukaci da a dakatar da dokar nan da ta haramta yin  kiwo barkatai da wasu jihohin kasar nan suka kafa.

 

Ministan tsaro Burgediya Janar Mansur Dan-Ali mai ritaya ne ya bayyana haka jim kadan bayan kammala wani taron sirri da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gudanar a fadar Asorok da ke Abuja.

 

A cewar sa dakatar da dokar a yanzu za ta taimaka gaya wajen dakile wasu matsalolin tsaro da ke addabar kasar nan.

 

Ministan ya kuma bukaci jami’an tsaro da su gaggauta gurfanar da wadanda aka kama suna da hannu cikin rikicin da ke faruwa tsakanin makiyaya da manoma gaban kotu.

 

Da yammacin jiya ne dai shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi wani taron sirri da shugabannin hukumomin tsaron kasar nan a fadar Asorok.

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 340,749 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!