ilimi
Gyaran aure: Muna dab da buɗe makarantar koyon zamantakewar aure a Hisbah – Ibn Sina
Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta ce, a watan Nuwamban 2021 ne sabuwar makarantarta ta koyar da zamantakewar aure za ta fara aiki.
Babban Kwamandan hukumar Malam Muhammad Haruna Ibn Sina ne ya bayyana hakan a wata zantawa da Freedom Radio.
Ibn Sina ya ce, a matakin farko zaɓi ne ga wanda ke da sha’awa, amma a nan gaba za su yi ƙoƙarin ganin an mayar da shi doka ga duk mai son yin aure a Kano.
“Kaso saba’in da biyar daga cikin korafin da muke karɓa kan matsalolin aure ne, wannan ne ya sanya muka samar da makarantar don bada horo”.
“Matsalar yawaitar mutuwar aure a kullum ƙaruwa ta k musmaman ma a Kano, don haka makarantar za ta samar da hanyoyin dabarun koyar da ilimin zamantakewar aure”.
Shugaban ya kuma ƙara da cewa za su shigar da ƙudiri gaban majalisar dokoki da zai tilastawa ma’aurata su shiga makarantar.
Muhamammad Harun ya kuma ƙara da cewa horaswar ba iya mata za ta tsaya ba hatta da maza za a basu damar shiga don samun daidaito.
You must be logged in to post a comment Login