Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Hadin kai tsakanin sarakuna zai kawo cigaba – Sarkin Kano

Published

on

Mai martaba sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya bukaci hadin kan sarakunan kasar nan da fahimtar juna kasancewar hakan zai kawo ci gaban al umma ta fannonin rayuwa daban-daban.

Alhaji Aminu Ado Bayero ya bayyana hakan ne a yayin da yake karbar bakuncin tawagar ‘yan majalisar masarautar Kaltingo da ke Jihar Gombe, bisa jagorancin mai martaba sarkin Kaltingo Injiniya Sale Muhammad Umar a fadarsa.

Sarkin na Kano ya ce irin wannan ziyara ta sarakuna tana karfafa dankon zumunci a tsakanin sarakuna da al’ummarsu.

A na sa jawabin mai martaba sarkin Kaltingo Injiniya Sale Muhammad Umar ya ce sun je fadar ta Kano ne da nufin karfafa dankon zumunci dake tsakanin Kano da Kaltingo mai tsohon tarihi.

Wakilinmu Muhammad Harisu Kofar Nasarawa ya rawaito cewa a yayin ziyarar sarkin na Kaltingo yana tare da wasu manyan ‘yan majalisarsa.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!