Connect with us

Labaran Wasanni

Champions League :  Lewandowsky ya fi kowa zura kwalaye a gasar ta bana

Published

on

Dan wasan kungiyar kwallon kafa na Bayern Munich Roberto Lewandowsky ya zama dan wasan da ya fi kowan ne dan wasa zura kwallo a kufin zakarun kungiyoyin kwallon kafar Turai na shekarar 2019/2020.

Lewandowsky dai ya zura kwallaye guda 15 a kakar wasanni ta zakarun turai a bana wanda hakan ya sanya ya fi kowanne dan wasa cin kwallon a gasar da aka karkare a ranar Lahadi.

Dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Juventus dan asalin kasar Potugal Cristiano Ronaldo ne dai  ya fi kowanne dan wasa yawan zura kwallo a kakar wasanni a gasar.

Ronaldo dai ya zura kwallaye 17 ne a kakar wasanni ta shekarar 2017/2018 lokacin yana bugawa kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid dake kasar Spaniya kafin sauya shekarsa zuwa kungiyar ta Juventus.

A bana dai dan wasan na Bayern Munich Roberto Lewandowsky ya ci kwallaye 55 a kakar wasanni ta bana.baki daya

 

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 335,289 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!