Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Ma’aikatan filin jirgin Aminu Kano sun nemi ɗaukin Shugaba Tinubu

Published

on

Wasu ma’aikatan hukumar filin jirgin saman Malam Aminu Kano, jihar Kano sun gudanar da zanga-zangar lumana da safiyar yau Asabar sakamakon wani gini da hukumar sojojin sama ke yi a wani fili da da ke gaban rukunin gidajen ma’aikatan watau Aviation Quarters.

Yayin zanga-zangar dai, jami’an sun buƙaci shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da shugaban rundunar sojin saman da majalisun tarayya har ma da sauran masu ruwa da tsaki da su sanya baki wajen dakatar da ginin.

A zantawarsa da manema labarai yayin gudanar da taron shugaban tsaro da walwalar ma’aikata na rukunin gidajen na Aviation Quarters Kwamared Zakariyya Muhammad Dauda, ya bayyana maƙasudin zanga zangar da cewa, sun fara ginin ne ba bisa ƙa’ida ba.

Haka kuma ya ƙara da cewa, sansanin sojin saman nan Kano, sun doki wani abokin aikinsu da bindnga lokacin da suke ƙoƙarin hana shi shiga gida domin ajiye iyalansa da ya ɗakko su daga makaranta wanda yanzu haka ya na kwance a asibiti.

Ya ce, ” Wannan fili namu ne, don kuwa mallakin hukumar filin jirgin sama ne kuma hukumar ce ma ta bai wa rundunar sojin saman filin da suka gina Barikinsu tare da makarantar koyon tuƙin jirgi, don haka ba su da ikon zuwa haka siddan su fara gine mana wurin da muke hutawa tare da motsa jiki mu da Ƴaƴanmu.”

Kwamared Zakariyya Muhammad, ya kuma ce, Sojoji da aka sanya gadin leburorin da ke haƙa a wannan fili domin toshe mana hanyar shiga gidajen mu sun yi mana barazanar harbi baya ga duka da suka yi wa ma’aikacinmu a kan ya nemi ba’asin cire mana alamar mallakar filin da muka yi.

Sai dai da Freedom Radio ta tuntuɓi Daraktan yaɗa labarai da hulɗa da jama’a na rundunar Sojin saman na ƙasa Air Commodore Edward Gabkwet wanda ya ce, zai bincika batun tare da magantuwa a nan gaba.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!