Labarai
Hajjin Bana: Akwai yiwuwar samun karin farashin kuɗin aikin Hajji- NAHCON
Hukumar kula da aikin hajji ta ƙasa NAHCON ta ce, akwai yiwuwar samun karin farashin kuɗin aikin Hajji a bana.
A cewar NAHCON hakan ya biyo bayan karin kudin masaukin alhazai da hukumomin ƙasar Saudiyya suka yi.
Rahotanni sun nuna cewa ƙasar Saudiyya ta rushe wasu daga cikin masaukan da alhazai ke sauka domin kawatasu da hakan ka iya shafar farashin masaukin da alhazan za su sauka a bana.
Cikin jihohin da abin zai fi shafa sun haɗa da Kano, Sokoto, Katsina, Kaduna, Bauchi, Kwara, Plateau.
A bana dai ana sa ran maniyyata daga Najeriya sama da miliyan 3 ne za su sauke farali, adadin da ya fi na shekarar 2022.
Da yake ƙarin haske kan lamarin Kwamishinan hukumar NAHCON mai kula da harkokin kudi da ma’aikata Alhaji Nura Hassan Yakasai, tabbatar da cewar cewa tuni tawagar su ta isa ƙasar Saudiyya don tattaunawa da mahukunta.
A cewar sa “Za mu tabbatar da alhazan Najeriya sun samu sassaucin farashi da masauki mai arha a hajjin bana”.
Sai dai ya buƙaci maniyyata aikin Hajjin bana da su yi shiri a kan lokaci don gujeea fuskantar ƙalubale.
You must be logged in to post a comment Login