Connect with us

Labarai

Hakimin Kumbotso ya dakatar da mai unguwa

Published

on

Hakimin Kumbotso Alhaji Ahmad Ado Bayero ya dakatar da mai unguwar Tudin Maliki, Abdullahi Yunusa bisa zargin sa da aikata zamba cikin aminci.

Ana dai zargi Malam Abudullahi Yunusa da karbar kudade a hannun matan karamar hukumar da niyyar za’a koyar da su sana’oin dogaro da kai.

Alhaji Ahmad Ado Bayero ya dakatar da mai unguwar ne yau a fadar sa dake garin na Kumbotso bayan tabbatar da laifin da ake masa na zargin mai unguwar da aikatawa ta bakin sakataran sa Abubakar Abdullahi.

Fadar shugaban kasa tayi magana kan sace hakimin Daura kuma sarkin dogarin Buhari

Sarkin Rano ya dakatar da wasu Hakimai

Sarkin Kano ya dakatar da mai Unguwar Badawa

Wakilin mu Kamilu Saminu Zawaciki ya rawaito cewa, hakimin Kumbotson ya bayar da umarnin nada Alhaji Alasan a matsayin sabon mai unguwar ta Tudin maliki na wucin gadi kafin a kammala bincike.

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 338,463 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!