Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Hanyoyin da Kwastam ta bi wajen kama harsasai a jihar Imo

Published

on

 Hukumar hana fasa-kwauri ta kasa ta sami nasara kama tarin harsasai da ya haura fiye da dubu biyar a jihar Imo dake kudancin kasar nan a  ya yin bukukuwan Kirismiti da na hutun karshen shekara.

Shugaban shiyya ta C na hukumar ta Kwastam  Yusuf Lawal ya sanar da haka  a ya yin da yake holin harsasan a  birnin Owerrin jihar ta Imo.

A cewar Yusuf Lawal hukumar ta sami nasarar kama harasasan ne tare da buhun  shinkafa ‘yar  waje da ya zarce dubu daya da kuma mota kirar Toyota Landcruiser jeep da harasashi bai huda.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewar a kwanakin baya hukumar ta irin wannan makamancin kame a jihar Kebbi.

An kama harsashen ne a cikin wata mota da ake zargin na haya ne inda aka boye su cikin kayan amfanin gida.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!