Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Za a fara daure masu adaidaita sahu kan goyon gefe – KAROTA

Published

on

Hukumar lura da zirga-zirgar ababen hawa ta jihar Kano KAROTA ta ce za ta rika daukar matakin hukuncin daurin watanni shida ko zabin tara ga duk direban adaidaitan sahun da aka samu da yin goyon gefe.

Jami’in yada labaran hukumar Nabulisi Abubakar Kofar Na’isa ne ya bayyana hakan, a zantawarsa da Freedom Radio.

Kofar Na’isa ya ce, hakan na cikin dokar hukumar ta KAROTA kuma za su tabbatar an yi aiki da ita domin yaki da bata gari.

Ba dai sabon abu ba ne a Kano yadda ake kai ruwa rana, tsakanin jami’an KAROTA da direbobin baburan adaidata sahun kan zargin karya dokokin hanya, batun da masu adaidaitar suka sha musantawa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!