Labarai
Har yanzu ba ga kwafin hukuncin kotu ba kan shari’ar Sanata Natasha- Majalisar Dattawa

Mai magana da yawun majalisar dattijai, Sanata Yemi Adaramodu, ya bayyana cewa har yanzu ba su karɓi kwafin hukuncin kotu na gaskiya ba, dangane da shari’ar da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta shigar.
Ta cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi, Adaramodu ya ce, majalisar ba za ta dauki wani mataki ba sai sun samu cikakken kwafin hukuncin daga kotun tarayya da ke Abuja, wanda aka yanke a ranar 4 ga wannan wata.
Ya kara da cewa babu wani sahihin umarni daga kotu da aka miƙa wa majalisar ko wata hukuma, don haka babu wanda zai iya aiwatar da abin da ya kira da “umarnin da ake zato” ko wasu bukatu da ba su da tushe a shari’a.
You must be logged in to post a comment Login