Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Har yanzu bamu kai ga tsayar da ranar kidaya ba: Hukumar kidaya ta kasa

Published

on

Hukumar kidaya ta kasa ta ce, har yanzu ba a kai ga fitar da ranar da za a fara kidayar jama’a a shekarar 2023 da muke ciki ba.

Shugaban sashin tsare-tsare da bincike na hukumar a nan Kano Alhaji Baba Balarabe Kabir ne ya bayyana hakan a zantawarsa da wakilinmu Nura Bello da safiyar yau, wadda tattaunawar ta mayar da hankali kan shirin fara kidayar jama’a.

Ya kuma ce, akwai bukatar mutane su baiwa jami’an kidayar hadin kai don samun nasarar aikin.

https://freedomradionig.com/wp-content/uploads/2023/02/LABARAN-RANA-HANTSI-CENSUS-15-02-2023.mp3?_=1

Shugaban sashin tsare-tsare da bincike na hukumar kidaya ta jihar Kano Alhaji Baba Balarabe Kabir kenan a zantawarsa da Freedom Radio.

Rahoton:Nura Bello

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!