Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Kotun koli ta dage karar da gwamnoni suka shigar kan CBN

Published

on

Kotun Kolin a Najeriya ta dage ci gaba da sauraron karar da wasu gwamnonin jihohin kasar nan suka shigar kan kalubalantar babban bankin kasa CBN na sanya wa’adin daina amfani da tsoffin kudi.

Kotun karkashin jagorancin mai shari’a John Okoro ta dage ci gaba da sauraron karar ne a zamanta na yau, inda ta sanya ranar 22 ga watan Fabrairun da muke ciki a matsayin lokacin yanke hukunci.

Gwamnoni goma ne dai suka shigar da karar da nuna bukatar kotun ta dakatar da babban bankin kasa CBN daga yunkurinsa na sanya wa’adin daina amfani da tsoffin kudin da ya sabunta.

Cikin gwamnonin akwai na jihar Kaduna, Kogi, Zamfara, Kano, Niger, Ondo, da Ekiti da dai sauransu.

Tuni dai mutane a kasar nan suka shiga ruɗani a kan ko za su iya ci gaba da amfani da tsofaffin takardun kuɗin, ko a’a, duk da umurnin da kotu ta bayar na jingine wa’adin 10 ga watan Fabrairu.

Haka zalika rahotanni daga wurare da dama sun nuna cewa bankuna sun daina karɓar tsofaffin takardun kuɗin, tare da kafa hujjar cewa umurni ne suka samu daga Babban Bankin kasa.

Rahoton:Madeena Shehu Hausawa

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!