Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Har yanzu Gwamnati ba ta bada kuɗaɗen gudanar da gasar wasanni ta ƙasa ba – Musa Ebomhiana

Published

on

Kwamitin shirye-shiryen gasar bikin kakar wasanni ta 2020, ya ce, kawo yanzu gwamnatin tarayya bata fitar da kudaden da tayi alkawarin baiwa jihar Edo don gudanar da bikin.

Shugaban gudanarwa kwamitin, Musa Ebomhiana ne ya bayyana hakan a birnin Benin dake jihar ta Edo.

Ya kuma ce, yayin da ya rage kwanaki kalilan a fara gudanar da gasar, izuwa yanzu gwamnatin bata saki kudaden ba.

“Duk da cewa gwamnatin jihar Edo na kyautata tsammanin za a fitar da kudaden amma da an fitar da kudaden a cikin lokaci da yafi dacewa,” a cewar Ebomhiana.

Haka kuma, ya ce, “biyan kudin akan lokaci zai taimaka wajen yin kyakkyawan shirye-shirye don gudanar da bikin a tsanaki.”

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!