Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Kano ce jiha mafi zaman lafiya a Najeriya – Tinubu

Published

on

Jagoran jam’iyyar APC na kasa Sanata Bola Ahmed Tinubu ya ce Kano ce jiha mafi zaman lafiya a Najeriya.

Madugun jam’iyyar ta APC ya bayyana hakan ne ya yin wani taron cikar sa shekaru sittin da tara da haihuwa wanda ya gudana a Kano a ranar litinin.

Tsohon gwamnan jihar ta Lagos ya kuma yabawa gwamnan Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje, wanda ya ce, ya yi namijin kokari wajen gudanar da ayyukan raya kasa.

‘‘Kano jiha ce mai dumbin tarihi da zaman lafiya sakamakon yadda gwamnatin Ganduje ta aiwatar da ayyukan raya kasa, idan ka samar da zaman lafiya za ka ga masu sha’awar zuba jari suna ta tururuwa zuwa jihar don gudanar da harkokin su’’ a cewar tsohon gwamnan jihar ta Lagos.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!