Kasuwanci
Har yanzu muna kan bakanmu na yajin aiki- NUPENG

Kungiyar Ma’aikatan dakon Man Fetur da Iskar Gas ta Najeriya NUPENG, ta ce za ta ci gaba da yin yajin aiki a fadin kasar biyo bayan gaza cimma matsaya da gwamnatin tarayya kan dakon man fetur da kamfanin Dangote zai fara zuwa gidajen Mai.
Shugaban NUPENG, Williams Akporeha, ya bayyana hakan a zantawarsa da tashar Talabijin ta Arise.
Taron da Ministan Kwadago da Ayyuka, Muhammad Dingyadi, ya jagoranta a jiya Litinin ya ƙare ba tare da nasara ba, sakamakon rashin jituwa kan batun kafa ƙungiyar direbobin tankuna a masana’antar ta Dangote.
Ya kuma ce ƙungiyar ba ta da wata mafita illa ta ci gaba da yajin aiki, bayan da ya zargi shugabancin Dangote da ƙin amincewa da ƙungiyoyin kwadago na man fetur, tare da ƙirƙirar wata ƙungiya ta daban ga ma’aikatansu.
You must be logged in to post a comment Login