Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Addini

Har yanzu muna nan a kan tuhumar da mu ke yiwa Sheikh Abduljabbar – Malaman Kano

Published

on

Zauren haɗin kan malamai da ƙungiyoyi na jihar Kano ya ce, har yanzu malamai suna nan a kan tuhumar da suke yiwa Sheikh Abduljabbar Kabara.

Hakan dai na cikin wata sanarwa ta saƙon murya da Babban Sakataren zauren Dr. Sa’id Ahmad Dukawa ya aike wa Freedom Radio.

Dukawa ya ce, “Sakamakon takunkumin da kotu ta ƙaƙabawa Abduljabbar kuma ba ta ɗage shi ba, hukumomi sun nusashshe mu cewa, zaman tuhumar da aka shirya ranar Lahadi ba zai yiwu ba”.

Ya ci gaba da cewa, “Amma Malamai suna nan a kan bakansu na tuhumar sa da zarar hukumomi sun bada izni”.

A ƙarshe zauren ya yi kira ga al’umma da su ci gaba da haƙuri, tare da bin umarni har zuwa lokacin da Allah zai ba da damar gabatar da zaman tuhumar.

Idan zaku iya tunawa, Zauren haɗin kan malamai da ƙungiyoyi na jihar Kano shi ne ya shigar da ƙorafi kan Malam Kabara a wajen Gwamnatin Kano.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!