Ƙetare
Hare-haren da Ukraine ta kai cibiyoyin makamashi sun jefa mazauna iyakar Rasha da Ukraine cikin duhu

Jami’ai a Rasha sun ce hare-haren da Ukraine ta kai kan cibiyoyin makamashi da jirage marasa matuƙa sun jefa mazauna yankunan da ke kan iyakar ƙasashen biyu cikin duhu.
Gwamnan yankin Belgorod Vyacheslav Gladkov ya ce fiye da mutum 20,000 ne ke zaune babu lantarki da na’urorin ɗumama gida.
Su ma gwamnonin Kursk da Voronezh sun bayar da rahoton hare-hare kan gine-gine da suka tayar da gobara a tashoshin lantarki.
Tun da farko ministan harkokin wajen Ukraine ya zargi Rasha da kai wa tashoshin lantarkin da ke samar wa tashoshin nukilya biyu wuta hari a ranar Juma’a da dare.
You must be logged in to post a comment Login