Connect with us

Labarai

Harin da aka kai wa gwamna Zulum ya yi sanadiyyar mutuwar sojoji 4 da ‘yan sanda 10

Published

on

Rundunar sojin kasar nan ta sanar da cewa jami’anta hudu da kuma ‘yan sanda goma aka kashe yayin kwanton bauna da ‘yan kungiyar Boko Haram suka yi tawagar gwamnan Jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum a ranar juma’ar da ta gabata.

Wata sanarwa da babban jami’in yada labaran rundunar tsaro ta kasa Manjo Janar John Enenche ya fitar, ta ce sun gano gawarwakin jami’an na su a daji ne sa’o’i 24 bayan harin da aka kaiwa jerin gwanon motocin gwamnan a kauyen Barwati a kan hanyarsu ta zuwa garin Baga.

Sanarwar ta kara da cewa tuni suka aike da kararrun jami’ansu masu gano inda aka binne nakiyoyi da sauran abubuwa masu fashewa domin kawar da su.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 340,259 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!