Labarai
Harin Kwara Ya Girgiza Najeriya — VP Shettima

Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, ya bayyana harin da aka kai wa al’ummar Woro da ke Karamar Hukumar Kaiama a Jihar Kwara a matsayin abin girgiza kasa, inda rahotanni suka nuna cewa akalla mutane 176 suka rasa rayukansu sakamakon harin ‘yan ta’adda.
Shettima ya bayyana hakan ne yayin ziyarar jaje da ya kai wa gwamnatin Jihar Kwara a ranar Asabar, inda ya danganta harin da bullowar wani sabon akidar addini da ba ta da alaka da tarihin yankin. Ya ce maharan sun kai farmaki daga karfe 5 na yamma zuwa karfe 3 na asuba, suna kashe mutane tare da kona gidaje, lamarin da ya tilasta wa daruruwan mazauna yankin tserewa zuwa Jihar Neja da makwabta.
Mataimakin Shugaban Kasar ya mika sakon jaje daga Shugaba Bola Ahmed Tinubu ga Gwamnan Jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, da al’ummar Kaiama baki daya. Ya jaddada cewa yankunan Kaiama da Baruten sun shahara da bin Musulunci cikin zaman lafiya da juna, sai dai wani bakon akida ne ya kawo tashin hankali a yankin.
Shettima ya kara da cewa rundunar sojojin Najeriya ta tura bataliya ta musamman zuwa yankin domin dakile barazanar tsaro da dawo da zaman lafiya. Haka kuma, Shugaban Kasa ya umurci Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA) da ta hada kai da gwamnatin jiha wajen tallafa wa wadanda harin ya shafa.
A nasa bangaren, Gwamna AbdulRazaq ya yaba wa Shugaban Kasa da Mataimakinsa bisa gaggawar daukar matakai, ciki har da tura sojoji da jami’an tsaro. Kungiyar Gwamnonin Kudu, Northern CAN, da tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki, duk sun yi Allah-wadai da harin tare da kiran a hukunta masu hannu a kisan. NEMA ta sanar da fara rarraba kayan agaji ga wadanda abin ya shafa.
You must be logged in to post a comment Login