Labarai
Hatsaniya ta barke a majalisar dattawa
Hatsaniya ta barke a majalisar dattawa a jiya biyo bayan gabatar da sakamakon rahoton kwamitin kula da hukumar zabe ta kasa INEC kan tantance mutanen da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya turo da sunayensu don nadasu a matsayin kwamishinoni a hukumar INEC.
Hatsaniyar ta fara ne lokacin da shugaban kwamitin Sanata Nazifi Gamawa, ya gabatar da sakamakon rahoton; inda ya bayyana cewa kwamitin bai amince a nada wakilin jihar Zamfara Ahmad Bello Mahmud don zama kwamishina a hukumar ta INEC ba.
Kammala jawabinsa ke da wuya, sai Sanata mai wakiltar mazabar Zamfara ta Tsakiya Kabiru Marafa, ya mike ya kuma zargi mambobin kwamitin da karbar cin hanci.
Ya ce yana da kwararan hujjoji da suka tabbatar masa cewa mambobin kwamitin sun karbi na goro daga wajen wasu mutane don kin amincewa da wakilin na jihar Zamfara.
Sanata Kabiru Marafa ya ma fito karara ya zargi gwamnan jihar ta Zamfara Abdul’aziz Yari da hannu dumu-dumu wajen baiwa mambobin kwamitin cin hanci don dakile yunkurin tantance Ahmed Bello Mahmud zama kwamishina a hukumar ta INEC.