Connect with us

Labaran Kano

Hisba ta yi karin girma ga manyan jami’anta

Published

on

Hukumar Hisba ta jihar Kano ta daga likkafar wasu jami’anta biyar zuwa matsayin masu taimakawa babban kwamanda na hukumar.

Jami’an da suka samu karin girmar sun hada da Malam Yahya Alhassan da Malam Abubakar Salihu Muhammad da kuma Malam Aminu Abdu.

Sauran sune Malam Sabo Awaisu da Malam Abdulladif Buhari wadanda hukumar ta yaba da jajircewarsu wajen gudanar da aiki tare kuma da daga likkafarsu zuwa matsayi na gaba.

Hakan na cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun jami’in hulda da ja’ama na hukumar Lawan Ibrahim Fagge wanda kuma aka rabawa manema labarai.

Sanarwa ta kuma ce sababbin kwamandojin biyar za su jagoranci shiyoyi biyar da ke masarautun jihar ta Kano da suka hada da: Kano da Rano da Gaya da Karaye da kuma Bichi.

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!