Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Kano

Mun halacci makarantar Shekara da ‘’Ya ”Yan Gwamna- Tsofaffin dalibai

Published

on

Shugabannin kungiyar tsofaffin daliban makarantar Sakandiren shekara da ke cikin birnin Kano sun bayyana cewa lokacin da makarantun gwamnati ke da daraja suna  halattar makarantar ne da ‘Ya ‘yan gwamnoni .

Shugabannin kungiyar daliban sun bayyana hakan ne lokacin da suka ziyarci filin Barka da Hantsi na nan Freedom Radio.

Hajiya Maryam Ibrahim Ringim da  Hajiya Saratu wadanda sune shugabannin kungiyar daliban makarantar ta Shekara sun ce a wancan lokacin sun yi aji da ‘’ya ‘’yan tsohon gwamnan jihar Kano Kanal Sani Bello mai ritaya.

Sun bayyana cewa a lokacin shi ne gwamnan jihar Kano mai ci.

Sunce sakamakon  habaka ilimi da gwamnatoci ke yi a lokacin suna makarantar Firamare sun  halacci aji daya da dangin gwamna mai ci da sauran ‘’ya ‘’yan manyan mutane na fadin jihar Kano.

Ilimantar da mata kamar ilimantar da al’umma ne- wani malamin addini

Hajiyar Maryam Ibrahim Ringim tace a yanzu kungiyar tsofaffin daliban makarantar ta shekara sun gina katafaren gurin shan magani na dalibai a makarantar a cikin abubuwan da kungiyar su ta tara daga tsofaffin dalibai.

Makarantar shekara an kafa ta ne a shekarar 1959 a matsayin makarantar Firamare daga bisani kuma ta koma makarantar Sakandire a shekarar 1979.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!