Labarai
Hisbah ta kama mutumin da ake zargi da safarar mata zuwa ƙasashen ƙetare

Hukumar Hisba ta jihar Kano ta samu nasarar kama wani mutum da yake kokarin yin safarar wasu mata zuwa wasu kasashen domin yin aikatau ko wasu abubuwan da basu da ce ba.
Mataimakin babban kwamandan hukumar Dakta Mujahiddin Aminudden ne ya bayyana hakan ta cikin wani sakon murya da ya raba ga manema labarai.
Dakta Mujahiddin ya ce ‘ya’ya mata amana ne a wurin iyayensu, a don haka yake kira garesu dasu sake saka ido akan su tare da basu nagartacciya tarbiya, don samar da al’umma ta gari.
Haka kuma ya bukaci iyayen da su tabbatar da cewa suna sauke nauyin da ya rataya a wuyansu na kula da iyalansu.
You must be logged in to post a comment Login