Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Kano

Hisbah zata bude sabbin ofisoshi a Kano

Published

on

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta bayyana cewa zata bude sabbin ofisoshi har guda uku (3) domin cigaba da ayyukan umarni da kyakykyawa da kuma hani da aikata mummuna.

Babban kwamandan hukumar Hisbah ta jihar Kano Sheikh Muhammad Harun Ibn Sina ne ya bayyana hakan ta cikin wani faifan bidiyo da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta na Facebook.

Sheikh Ibn Sina ya ce gwamnatin jihar Kano ta baiwa hukumar Hisbah sabbin ofisoshi na din-din-din a rukunin gidajen Khalifha Isaka Rabi’u da na Sheikh Ja’afar Mahmud Adam, da kuma rukunin gidaje na Sheikh Nasiru Kabara.

Kazalika Ibn Sina ya ce daga gobe Litinin 13 ga watan Janairu da muke ciki ne sabbin ofisoshin za su fara aiki.

Labarai masu alaka:

Hukumar Hisba ta Kano ta kulla alaka da cibiyar Hisba ta Saudi Arabiya

Hisbah bata da hurumin yin bulala ko cin tara ga mai laifi -Barista Sunusi Musa

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!