Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Bai kamata ‘yan Arewa su rika tsoron kafa ‘yan sandan jihohi ba –AIG Hadi Zarewa

Published

on

Masani a harkar tsaro AIG Hadi Zarewa mai ritaya yace bai kamata yankin Arewacin kasar nan su rika jin tsoron kafa ‘yan sandan jihohi ba, domin zai kawo karshen matsalar barazanar tsaro da wasu jihohin Najeriya ke fuskanta a yanzu.

AIG Hadi Zarewa mai ritaya ya bayyana hakan ne ta cikin shirin Muleka mu gano na musamman da ya mayar da hankali kan batun samar da jami’an sintiri na Bijilanti da wasu gwamnonin kudancin kasar nan ke shirin yi.

Hadi Zarewa mai ritaya ya kuma yi kira ga al’ummar yankin Arewacin kasar nan dasu daina tsoro ko shakku kan batun kirkiro ‘yan sandan jihohi domin hakan mafita ce ga al’umma baki daya musamman ta fuskar samar da ingataccen tsaro a jihohin Najeriya.

Alhaji Hadi Zarewa mai ritaya ya nanata cewa mutane su daina zaton Gwamnonin jihohin kasar nan zasu mayar da ‘yansan dan jihohin tamkar ‘yan amshin shata, ko su sanya su cikin Aljihu domin doka ba zata zuba ido suna amfani dasu wajen biya musu bukatunsu da suka saba doka ba.

Wakilin mu Abdulkarim Muhammad Abdulkarim Tukuntawa daya bibiyi yadda shirin ya gudana ya rawaito Hadi Zarewa mai Ritaya na cewa Najeriya na fuskantar karancin jami’an tsaro a don haka samar da ‘yan sandan jihohi shine kadai mafita wajen magance duk wata barazanar tsaro a wasu daga cikin jihohi, kamar yadda sauran kasashen da suka cigaba na duniya keyi.

Labarai masu alaka:

Bamu cafke Ali Kwara ba -‘Yan Sanda

Kai tsaye : Wasu hotunan shugaban kasa da sarakunan Kano a jami’ar horar da ‘yan sanda a Kano

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!