Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Addini

Huɗuba: Zagin shugabanni ne ke ƙara jefa mu a matsin rayuwa – Dakta Abdullahi

Published

on

Limamin masallacin juma’a na Umar Sa’id Tudunwada da ke Tukuntawa anan Kano Dakta Abdullahi Jibrin Ahmad ya ce, zagin shugabanni ne ke haifarwa ƙsar nan koma baya.

Dakta Abdullahi Jibrin Ahmad ya bayyana hakan a huɗubar sa ta sallar Juma’a.

Dakta Abdullahi ya ce “A wannan lokacin da ake cikin tsadar rayuwa ba wai yawan zagin shugabannine zai magance wannan matsalar ba illa al’umma su rinka addu’a da kuma hakuri”.

“A yanzu haka al’umma sun fi yawaita faɗar baƙaƙen maganganu a kan shuwagabanni ba wai neman zaɓi daga ubangiji ba, don haka ya kamata al’umma su koma ga Allah da kuma kyautata zato ga shugabanni” a cewar Dakta Abdullahi.

Dakta Abdullahi Jibrin Ahmad ya kuma ce dukkan masu haƙuri makomarsu na gobe alƙiyama domin ubangiji yayi albishir gare su.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!