Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Addini

Hudubar sallar juma’ar limaman Kano a yau ta mayar da hankali ne kan zakkar fidda kai

Published

on

Mafi-akasarin limaman masallatan sun mayar da hankali ne kan batun zakkar fidda kai, wadda ake fitarwa a cikin kwanakin karshe na watan Ramadan.

 

A hudubarsa, limamin masallacin Juma’a na Zam-Zam dake Hotoro Gwani Zubair Hamza, ya bukaci al’umma da su fitar da Zakkatul fitr kamar yadda addinin musulunci ya umarta.

 

A ta sa hudubar limamin masallacin juma’a na Mukhtar Abbas dake Unguwar Farm Centre Malam Usman Adamu Kurna, ya bukaci al’umma da su dage wajen ribatar ragowar sauran kwanakin da suka rage na watan Ramadan.

 

Shi kuwa limamin masallacin juma’a na Kuyan ta Inna Malam Muhammad Aminu, kira ya yi ga al’umma da su rike darasin da suka koya a watan Ramadan, kuma su yi aiki da shi, kamar yadda wakilinmu Sani Ahmad Sagagi ya rawaito mana.

 

Limaman dai sun bukaci mawadata da su ci gaba da tallafawa marasa galihu dake cikin al’umma.

 

 

 

 

 

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!