Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Hukumar AIB ta gabatar da rahoto akan hadarin da ya faru na jirgin soji da ya yi sanadiyar mutuwar hafsat soja

Published

on

Hukumar binciken hadurra ta kasa AIB ta gabatar da rahoton wucin gadi kan hadarin da ya faru na jirgin soji da ya yi sanadiyar mutuwar tsohon babban hafsan sojin kasar nan Laftanar Janar Ibrahim Attahiru.

Hakan na cikin sanarwar da ta fito daga ofishin jami’in yada labaran hukumar, Tunji Oketumbi, jiya a Legas.

Ta cikin sanarwar shugaban hukumar, Akin Olateru, ya ce hukumar ta mika rahoton wucin na gadi kan hadarin ga babban hafasan sojin saman kasar nan bayan kusan watanni uku na binciken.

Masu binciken sun lissafa matakai 27 da hanyoyin kariya guda 8 da za’a bi domin kiyaye afkuwar hakan a nan gaba.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!