Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kiwon Lafiya

Hukumar aikin Hajji ta kara wa’adin rajistar maniyyatan Hajjin bana

Published

on

Hukumar aikin Hajji ta Najeriya NAHCON ta kara wa’adin rajistar maniyyatar Hajjin bana.

Tun da fari dai hukumar ta NAHCON ta sanya wa’adin gobe Asabar 31 ga watan Maris a matsayin ranar karshe da zata kammala rajistar maniyyatan na bana.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da wata jami’ar hukumar Fatima Mustapha ta fitar ranar Alhamis din da ta gabata a Abuja.

A cewar sanarwar a yanzu hukumar za ta kara wa’adin rajistar zuwa karshen watan Aprilu mai kamawa.

Fatima Mustapha ta cikin sanarwar ta kuma ce, za a samu bambanci wajen adadin kudin hajjin da maniyyata za su biya a bana.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!