Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kiwon Lafiya

Hukumar NDLEA ta kama mutane 2 bisa zargin su da safarar miyagun kwayoyi

Published

on

Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA ta damke wasu mutane biyu da take zargi da safarar muggan kwayoyi a garin Onitsha na Jihar Anambra.

Hukumar ta kama Solomon Michael da bisa zargin safarar tabar wiwi yayin da ta damke Okechukwu Udenkwo bayan samunsa da Hodar Ibilis wato Cocaine.

A zantawarsa da manema labarai a garin Awka, babban kwamandan hukumar na Jihar ta Anambra Sule Momodu ya bayyana cewa Solomon Michael ya kware wajen dillancin tabar wiwi a garin Onitsha, yayin da Okechukwu Udenkwo kuma ya kware cikin safarar Hodar Ibilis a Nando.

Sannan ya kuma nemi hadin kan shugabannin al’ummar yankunan Jihar baki-daya, musamman ma wajen sanar da hukumar da zarar sun samu labarin bullar muggan mutane masu safarar miyagun kwayoyi.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!