Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kasuwanci

Hukumar Anti-corruption ta bankaɗo gurɓatacciyar masara a kasuwar Dawanau

Published

on

Hukumar karɓar ƙorafi da yaƙi da cin hanci da rashawa ta jihar Kano ta kama wasu mutane da suka shigo da gurɓatacciyar masara.

Shugaban hukumar Barista Mahmud Balarabe ne ya bayyana hakan ga Freedom Radio.

Ya ce “Mun samu bayanin sirri na shigowar wata tirela maƙare da masara mai guba da ta shigo Kano a kasuwar Dawanau wadda ake ƙoƙarin niƙawa don sayarwa ga jama’a”.

Barista Balarabe ya kuma ce “mun samu nasarar kama mutane biyu da suke da alaƙa da mai masarar, a daidai lokacin da suke ƙoƙarin shiryata don fitar da ita zuwa wasu sassan”.

Shugaban ya ce, tuni sun miƙa lamarin ga ƴan sanda don faɗaɗa bincike, kuma za su zauna da shugabannin kasuwar don gano bakin zaren.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!