Labarai
Hukumar CAC za ta dakatar da masu sana’ar POS marasa rajista daga Janairun 2026

Hukumar Rijistar Kamfanoni ta Najeriya CAC ta sanar da cewa daga ranar 1 ga Janairu 2026 za ta fara rufe dukkan masu gudanar da ayyukan POS da ba su yi rijista da hukumar ba
Hukumar ta ce yawan masu POS da ke aiki ba bisa ka’ida ba yana karuwa wanda ya saba wa CAMA 2020 da kuma dokokin CBN na Agent Banking Regulations
A cikin sanarwar da ta fitar ranar Asabar CAC ta ce duk mai POS dole ne ya yi rijista ko kuma a rufe shi nan take tare da umartar jami’an tsaro su tabbatar da bin doka a fadin kasar
Hukumar ta zargi wasu kamfanonin fintech da taimaka wa ayyukan POS marasa ka’ida wanda ke jefa tsarin kudi da dukiyar al’umma cikin hadari
CAC ta bayyana cewa duk POS/terminals da ba’a yi wa rijista ba za a kwace su ko a rufe su gaba daya
Duk Manhajar hada-hadar kudi ta yanar gizo da ke mara wa ayyuka zamba baya za a saka ta cikin jerin shafukan da za’a kai rahotonta ga CBN.
Sanarwar ta shawarci duk masu ayyukan POS su yi rijista nan da nan domin gujewa hukuncin da zai biyo bayan take dokar.
You must be logged in to post a comment Login