Kasuwanci
Hukumar CREDITCORP ta kaddamar da shirin wayar da mutane muhimmancin karbar bashi marar Lamuni

Sabuwar hukumar samar da lamuni ga masu amfani da Kayayyaki ta Najeriya CREDITCORP, ta kaddamar da shirin wayar da kan Al’umma kan muhimmanci karbar bashi marar Ruwa.
Taron wanda ya gudana Kano a rufaffen dakin filin wasa na Sani Abacha, ya yi duba kan aiyyukan sabuwar hukumar musamman ma ta fannin bayar da basussukan.
Ya yin gudanar da taron na wayar da kan al’umma kan muhimmancin karbar bashin wanda babu Lamuni, shugaban hukumar ta CREDITCORP, Uzoma Nwagba ya ce an samar da tsarin ne karkashin shirye shiryen shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu, domin bawa Al’ummar kasar damar samun kayayyakin bukatu da aiyyuka ba tare da wahalar tara Kudi na dogon Lokaci ba.
Da ya ke jawabi a madadin bankunan da suka halarci taron wajen da suka hada da Ecobank sai ALT da Fidelity, shugaban Bankin na Ecobank Muhammad Mustapha Manye ya yi karin haske kan tsare tsaren hadakar da ke tsakanin Bankuna da hukumar.
A nasa jawabin shugaban hadaddiyar kungiyar Kasuwar Kantin Kwari Musa Umar Sanda Arzai, ya ce ‘yan Kasuwar su Sunyi Murna da Sabon tsarin Kuma zai taimaka musu matuka.
Shi ma babban daraktan a ma’aikatar kasuwancin ta jihar Kano , da ya wakilci Kwamishinan Kasuwanci Shehu Wada Sagagi, da gwamnatin jihar Kano , Alhaji Ibrahim Kabara , ya ce gwamnatin jiha a shirye take ta shiga cikin tsarin don tabbatar da ci gaban sa, da alfanun sa ga al’ummar jihar.
Sabon tsarin dai ya samar da hanyoyin bada bashin , siyan Mota , Babur da Hasken Wuta na Solar da sauran ababen more rayuwa.
You must be logged in to post a comment Login