Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kiwon Lafiya

Hukumar CUSTOM: ta kama mota makare da maganin Codeine na kimanin naira miliyan 240

Published

on

Hukumar yaki da fasakwauri ta kasa wato CUSTOM ta kama wata motar dakon kaya makare da maganin tari na Codeine wanda darajar kudin su ya kai naira miliyan dari biyu da arba’in.

A cewar hukumar jami’an ta da ke jihar Lagos ne suka samu nasarar kama motar kirar DAF mai dauke da lamba LSR 944 XF a babbar titin Mile 2 zuwa Oshodi.

Babban kwanturola mai kula da yankin na Oshodi Aliyu Muhammed ya ce motar makare ta ke da katan din maganin tarin na Codeine guda dari shida.

Sai dai ya ce, suna kan bincike, domin kuwa har ya zuwa lokacin da ya ke zantawa da manema labarai, ba su kai ga gano inda motar za ta kai kayan ba.

Ya kuma ce, direban motar ya tsere lokacin da ya hango jami’an hukumar ta kwastam lamarin da ya sa kenan suka kasa gano inda za a kai maganin.

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!