Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kiwon Lafiya

Fadar shugaban kasa ya mayar da martani ga shugaban cocin Katolika

Published

on

Fadar shugaban kasa ta mayar da martani ga kalubalantar da shugaban Cocin Katolika shiyyar Yola Stephen Mamza ya yi ga shugaban kasa Muhammadu Buhari na cewa, ba ya yin abinda ya da ce, kan rashin tsaro da ke addabar kasar nan.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai Malam Garba Shehu.

Ta cikin sanarwar, fadar shugaban kasa, ta zargi shugabannin al’umma da laifin kara rura wutar rikice-rikice da ake samu a sassa daban-daban na kasar nan.

A cewar Malam Garba Shehu ta cikin sanarwar dai, gwamnatin shugaba Buhari ta na aiki dare ba rana don tabbatar da tsaro da kuma rayukan al’umma.

A baya-bayan nan ne dai shugaban Cocin Katolika Shiyyar Yola Stephen Mamza, ya zargi shugaban kasa da rashin katabus game  da yawan rikice-rikice da ake samu a kasar nan.

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!