Labarai
Hukumar DSS ta gurfanar da Abdulazeez Obadaki bisa zargin jagorantar harin ta’addanci

Hukumar tsaro ta DSS ta gurfanar da Abdulmalik Abdulazeez Obadaki, wanda ake zargi da zama babban jagoran harin ta’addanci da aka kai wa majami’ar Deeper Life Bible da ke na jihar Kogi, a shekarar 2012.
A safiyar ranar 7 ga Agusta, 2012, wasu mutane uku dauke da bindigogin AK-47 suka buɗe wuta kan masu ibada a majami’ar.
Nan take mutane 15 suka rasa rayukansu, yayin da wasu hudu suka mutu daga baya sakamakon raunukan da suka samu.
Tun a wancan lokacin aka alakanta harin da kungiyar Ansaru tsagin Boko Haram, wanda ya jikkata da dama bayan wadanda suka mutu.
Bayan harin cocin Okene, rahotanni sun ce Obadaki ya jagoranci wata kungiyar da ta kai hare-hare kan bankuna biyar a Uromi, Jihar Edo, inda aka kashe mutane tare da kwashe kudade masu yawa.
Daga bisani jami’an tsaro suka cafke shi suka ajiye shi a gidan yari na Kuje, amma ya tsere a lokacin da aka balle gidan yarin a watan yulin 2022.
A ranar 15 ga Nuwamba, 2025, DSS ta sanar da sake cafke Obadaki bayan an kamo shi a matsayin jagoran Ansaru da ya tsere.
You must be logged in to post a comment Login