Labarai
Hukumar EFCC na zargi tsohon babban daraktan hukumar NEMA
Hukumar EFCC mai yaki da cin hanci da rashawa ta zargi tsohon babban daraktan hukumar bada agajin gaggawa ta kasa NEMA da wasu daraktoci 6 na hukumar da hannu cikin almundahanar kudi Naira biliyan biyu da rabi.
Hukumar ta EFCC ta ce tana sa-ran daraktoci shidan za su bada gamsassun bayanai yayin binciken da su ke, kuma NEMA ta kasance karkashin Ofishin mataimakin shugaban kasa.
Baya ga tsohon babban daraktan NEMA Sani Sidi Muhammad, sauran daraktocin da EFCCn ke zargi da badakalar sun hadar da daraktan kudi da ajiya Akinbola Hakeem Gbolahan da daraktan ayyuka na musamman Mista Umesi Emenike, da kuma daraktan takaita aukuwar iftila’i Malam Ahassan Nuhu.
Sauran su ne jami’i mai kula da sashen sufurin sama da motocin agaji Mamman Ali Ibrahim, babban jami’in kula da kayayyaki Ganiyu Yunusa Deji, sai kuma daraktan walwala Kanar Muhammad.
Rahotanni na nuni da cewa a gobe ne mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo zai gana hukkumar gudanarwar NEMA don tattauna wannan rahoto da kuma bincike na EFCC domin daukar mataki na gaba.