Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Yan kunar bakin wake 3 sun mutu a harin Muna Garage

Published

on

‘Yan kunar bakin-wake uku ne su ka mutu tare da jikkata wasu mutanen bayan hare-haren da su ka kai yankin Muna Garage da ke birnin Maiduguri na Jihar Borno, a daren Juma’ar da ta gabata.

Tsohon shugaban hukumar bayar da agajin gaggawa ta Jihar Borno, SEMA, kuma shugaban kwamitin da ke kula da ayyukan agaji a Jihar ta Borno Engr. Satomi Ahmad ya shaida wa manema labarai cewa hare-haren an kai su ne daban-daban har sau uku.

Ya ce jami’an agaji da na tsaro sun kai dauki ga wadanda suka samu raunuka inda aka garzaya da su asibiti.

Jami’in ya kuma ce abun ya faru ne da kusan karfe 9:30 na dare, ko da yake kafin sannan da wajen misalin karfe 7:00, lokacin sallar Magariba, an rika jin kararraki, wadanda ake gani ko na makaman atilare ne na soji.

Rahotanni sun ce bayan kai harin abubuwa sun lafa, mutane suka ci gaba da gudanar da harkokinsu, kafin zuwa lokacin dokar hana fita ta dare wadda ke aiki daga karfe goma da rabi na dare a birnin, ko da yake yankin da abin ya faru suna da lokacinsu na dokar daban, kasancewar yankin na bayan gari ne.

Wannan dai shi ne karo na kusan 13 da ake kai harin kunar bakin-wake a yankin na Muna Garage, kuma na biyar a cikin wannan shekarar ta 2018.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!