Labaran Kano
Hukumar EFCC ta cafke masu kamfanin boge da bindigu a Kano
Hukumar yaki da cin hanci da rashawa EFCC ta kama wasu mutane biyu a
nan Kano masu suna Garba Iliyasu da Umar Iliyasu da ke gudanar da
kasuwancin zamani da ake yi wa mutane romon baka mai taken Ponzi
Scheme karkashin MGB Global Market.
Kamen na su ya biyo bayan bayanan sirri da hukumar ta tattara game da
yadda suke damfarar mutane bayan sun yi musu dadin bakin cewa akwai
gwaggwabar ribar akalla kashi 50 cikin makonni biyu da shiga kasuwancin.
Wannan dai na kunshe ne cikin wata sanarwa da babban jamiin yada labaran
hukumar Wilson Uwujaren ya fitar a yau Juma’a.
Wilson Uwujaren ya yi karin hasken cewa a lokacin da suka kama mutanen
sun kwato na’urorin kwamfiyuta da na cirar kudi wato POS da kuma wasu
takardu.
Sanarwar ta kara da cewa binciken EFCCn ya gano cewa wani mai suna
Muhammad Garba Iliyasu wanda shi ne manajan daraktan kamfanin ya
tsere, sai wasu ‘yan uwansa guda Abubakar Garba Iliyasu da Ibrahim Garba
Iliyasu da suma suka tsere, ana kuma ci gaba da nemansu.
Bayan wani samame da hukumar ta gudanar a gidan mutanen da ke Hotoro
a nan Kano, ta gano wasu bindigogi da alburusai da kuma takardun da ke
da alaka da aikata muggan laifuka.