Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Hukumar FRSC ta yi ƙarin girma ga jami’anta 445

Published

on

Hukumar kiyaye abkuwar haɗura ta ƙasa, ta yi ƙarin girma ga wasu manyan jami’anta 445.

Jami’in yaɗa labaran hukumar Bisi Kazeem ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwar da ya fitar jim kaɗan bayan wani taron da hukumar ta gudanar.

Shugaban hukumar Barista Bukhari Bello, ya ce waɗanda aka ƙarawa girman sun haɗar da manyan mataimakan kwamandojin kula da manyan hanyoyi guda 264 zuwa manyan kwamandoji.

Sai kuma ƙananan mataimakan kwamandojin kula da manyan hanyoyi da aka ƙara musu girma zuwa manyan mataimaka su 181, tare da bukatar su da su ƙara ƙaimi wajen kiyaye abkuwar haɗura a kan hanyoyin ƙasar nan.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!