Connect with us

Labarai

Shugaba Buhari ya yi ganawar sirri da babban sufeton ‘yan sanda Ibrahim Idris

Published

on

Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi wata ganawar sirri da babban sufeton ‘yan sandan Najeriya Ibrahim Idris yau juma’a, a fadar Villa da ke Abuja.

Rahotanni sun ruwaito cewa har yanzu ba’a yi wani bayani ba kan abubuwan da suka tattauna a kai, wanda suka kammala da misalin karfe 2:35 na rana.

Wannan na zuwa ne bayan kwana guda da lokacin ritayar babban sufeton ‘yan sandan, da ya kamata ya yi jiya 3 ga watan Janairu, inda zai cika shekaru 60 da haihuwa ranar 15 ga wata.

Akwai dai rade-radin cewa shugaban kasa Mauhammadu Buhari ka iya kara wa shugabancin babban sufeton ‘yan sandan wa’adi, a wani bangare na tsaurara matakan tsaro a babban zaben kasar nan da zai gudana a watan gobe.

Rahotanni sun bayyana cewa babbar jam’iyyar hamayya ta PDP na ciagaba da sukar wannan mataki, da ke cigaba da yaduwa a kafafen sada zumunta da kuma na yada labarai.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 341,026 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!