Connect with us

Labarai

rundunar sojin Najeriya ta kashe mayakan Boko Haram 6 a wani simame

Published

on

A jiya Juma’a rundunar sojojin Najeriya ta tabbatar da kashe mayakan kungiyar Boko Haram su 6 a yayin wani simame da rundunar ta kai, da nufin tarwatsa maboyar mayakan ‘yan ta’addan dake shiyyar arewa maso gabashin kasar.

An dai hallaka ‘yan ta’addan ne bayan da dakarun sojojin suka lalata maboyarsu dake kauyukan Gawa da Boskoro a jihar Borno a ranar tun a ranar Alhamis din da ta gabata.

A cewer rundunar sojin tas kuma kubutar da wasu mata uku da ake zargin yan book haram din sunyi garkuwa da su a kauyen Boskoro.

Tuni aka kai matan uku da aka kubutar zuwa sansanin tsugunar da ‘yan gudun hijira dake Borno.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!