Labarai
Hukumar hajji ta Najeriya ta rage kudin aikin hajji na bana
Hukumar aikin hajji ta kasa NAHCON ta rage naira dubu 51, 170 a cikin kudaden da ta ayyana tun da fari a matsayin kudin aikin hajji bana.
Wannan na kushe ne cikin wata sanarwa da jami’ar hulda da jama’a ta hukumar Fatima Sanda Usara ta fitar da yammacin jiya aka rabawa manema labarai a birnin tarayya Abuja.
Ta cikin sanarwar hukumar ta kuma umarci dukkanin hukumomin jin dadin alhazai na jihohi da su gaggauta mayar wa da maniyyatan kudaden da aka rage musu.
Ta ce ragin ya samo asali ne bayan da aka sake yin nazari kan hanyoyin da alhazan kasar nan ke ta’ammuli da su a kasar ta Saudiyya aka kuma samu wasu mafi sauki lamarin da ya sanya kasar ta Saudiyya ta rage kudin mota.
Haka zalika hukumar ta NAHCON ta kara wa’adin lokacin rufe karbar kudin aikin hajjin na bana da ya kamata a ce an rufe tun a ranar juma’ar da ta gabata zuwa 15 ga watan Yuli.
A cewar hukumar hakan zai taimakawa maniyyatan damar biyan kudaden su a saukake, inda kuma ta yi kira ga wadanda basu cika kudaden su ba da suyi kokari su cika.